IQNA

A Sudan An kame Sojoji  9 Bisa Zargin Kisan Fararen Hula

19:52 - August 02, 2019
Lambar Labari: 3483904
Bangaren kasa da kasa, an kame sojoji 9 da ake zargin suna da hannua  kisan da aka yi wa fararen hula garin Umdurman.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kakakin majalisar sojojin kasar Sudan Laftanar Jana Shams El Din Kabbashi, ya ce tuni aka kori wasu sojoji guda tara na rundunar agaji gaggawa ta RSF ta kasar da kuma ci gaba da tsare su saboda zargin da ake musu da hannu cikin rikicin baya-bayan nan da suka faru a garuruwan Omdurman da El-Obeid.

Janar Kabbashi ya bayyana hakan ne a yau juma’a inda yace ba ya ga wannan mataki na kora da kuma ci gaba da tsare sojojin, har ila yau kuma ya ce gwamnan jihar arewacin Kordofan da kuma majalisar tsaron jihar su ne suke da alhakin abin da ya faru din na kashe wasu mutane 6 ciki kuwa har da wasu yara ‘yan makaranta su 4 a garin na El-Obeid a ranar Litinin din da ta gabata.

A jiya ne dai dubun dubatan ‘yan kasar Sudan din suka fito kan titunan garin Omdurman din don nuna rashin amincewarsu da wannan kisan gillan lamarin da yayi sanadiyyar kashe wasu mutane 4 da kuma raunana wasu da yawa sakamakon bude musu wuta da jami’an tsaro suka yi.

Har ya zuwa yanzu dai lamurra ba su daidaita ba a kasar ta Sudan tun bayan kifar da tsohuwar gwamnatin Umar al-Bashir da sojoji suka yi.

3831806

 

 

captcha